25/11/2023
Mu Girmama Malamai Ko da Muna da Saɓani da Su.
A wannan zamani da yawa daga ɗaliban ilmin, an samu ilmin ne kawai amma an rasa tarbiyyar ilmin, da mun ga malam wane ya saɓawa malam wane a wata fuska ta ilmi ko usulubi da yake bi wajen isar da sako ta saɓa ma hankali, sai mu kuma mu fito tare da munanan lafazin da suke tare da cin mutunci gare shi da sunan raddi ko bada kariya ma wanin mu.
Lallai ne yana da kyau, mu mutunta mutane da s**a ɗara mana a shekaru, musamman ma Maluma k**ar yadda hadisi yake cewa:
An ƙarɓo daga Ubaidah bin Samit yana cewa, Manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: "Duk wanda baya mutunta manyan mu, baya tausaya ma ƙananan mu, kuma bai san haƙƙin malaman mu ba, to, wannan ba shi a cikin al'umma ta".
Imam Ahmad ne ya rawaito wannan hadisin daga Ubaidah bin Samit a cikin Musnadul-Ansar hadisi mai lamba 21693.
Shehun Malami Ɗawus bin Kaisan yana cewa: "Yana daga cikin Sunna a darajanta mutane huɗu, Malami, da tsoho mai furfura, da Sarki, da Mahaifi"
Albagwi ya kawo shi cikin Sharhus-Sunnah.
In fa ance mahaifi ba fa sai naka mahaifin ba, mahaifi suna ne gama gari na duk wanda ya haihu ba sai wanda ya haife ka ba, don cin mutuncin mai iyali cin mutuncin iyalansa ne.
Don haka, wajibcin Musulmi ne ya darajan ta Malami, ya mutunta shi, ya yi ladabi wajen ambaton sunan sa tare da yi masa addu'ar samun rahama da gafara daga Allah, ko malamin yana raye ne ko bayan ya mutu, kuma ba sai wanda kake so ba kawai, musamman in ya kasance fitacce ne wajen taimako gaskiya da yaɗa Sunna da tozarta ƙarya da tarwatsa ta.
Shehun Malami Abu Zur'ah Ar-Razi yana cewa: "Ina tare da Imam Ahmad bin Hambaliy sai aka ambaci sunan Ibrahim bin Ɗuhman, ɗaya daga cikin malamai na Allah, a lokacin shi Imam Ahmad ba shi da lafiya yana kwance amma nan take sai ya tashi ya zauna, ya ce, bai k**ata a ambaci mutanen kirki mu kuma muna kwance ba".
Tahzib Al Tahzib (1/148).
Allahu Akbar! Ka ji fa yadda magabata suke girmama malamai a gabannin idanun su da bayan su.
Allah Ka sa mu dace, Ka yafe mana kura-kuran mu.
Abu Abdir-Rahman Al-Fullaty!
11/Jumada ula/ 1445 Hijira.
25/11/2023 Miladiyya.