AK Ammar kano

AK Ammar kano Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from AK Ammar kano, Lagos.

24/04/2025
π—žπ—’π—ͺπ—”π—‘π—˜ 𝗗𝗔𝗑 𝗔𝗗𝗔𝗠 π— π—”π—œ 𝗗𝗔π—₯𝗔𝗝𝗔 π—‘π—˜Kowanne Dan adam da ka gani mai Daraja ne, mai gadin gidanku, ko Direban gidanku, ko Almaji...
15/05/2024

π—žπ—’π—ͺπ—”π—‘π—˜ 𝗗𝗔𝗑 𝗔𝗗𝗔𝗠 π— π—”π—œ 𝗗𝗔π—₯𝗔𝗝𝗔 π—‘π—˜

Kowanne Dan adam da ka gani mai Daraja ne, mai gadin gidanku, ko Direban gidanku, ko Almajirin gidanku ko 'yar aikin gidanku dukkaninsu suna yi ne don su rufawa kansu asiri, suna yi ne don kaucewa cin mutunci da gorantawa, suna yi ne don gujewa daukar kayan wani.
-
Sai dai Kash! a yanzu da yawanmu mu dauki gori, cin mutuncin na kasa da mu da masu karamin Karfi wadanda suke da bukatar taimakonmu ba abakin komai ba, duk abinda ka ga mutum yana yi madamar ba sata ka ga yanayi ba indai har neman halalinsa yake to idan kana da halin taimakonsa ka taimakeshi idan babu to bai kuma dace ka wulakantashi kawai don Allah ya kaddara zamowarsa ko zamowarta a karkashinku ba.
-
A wannan yanayi da aka tsinci kai ciki, kar ka yi mamaki don ka ga makwabcinka yana dako ko leburanci, ko gadi, rayuwarce ta zamo haka wadanda suke da damar su tallafa masa musamman makwabtansa masu hali sun ki to hakan ba zai zamo abin cin mutuncinsa ko aibatashi cikin Al'umma ba, kai baka bashi ba, kuma baka yi masa hanyar da zai samu ba yana buge-bugensa don rufawa kansa asiri ka zo kana yi da shi cikin Al'umma shin kai kana da tabbacin dorewar arzikinka.
-
Mace ce Mijinta ya mutu ya bar mata 'yaya da yawa babu mai tallafa mata sai Allah, ta Dan samu tana Aiki a wani gidan don ciyar da marayun da take dasu kai baka taimaketa ba, kuma baka taimaki yayanta ba don me yasa zaka rinka shiga cikin mutane kana cewa taki Aure ko ga abinda take? kai kana da tabbacin dorewar rayuwarka? idan yanzu ka mutu wa kake tunanin zai kula da dawainiyarsu? idan baka da Aure shin ya kake tunanin makomar na kanwarka?
-
Duk Mutumin da ka gani karka taba Raina shi babu mamaki ya fika kima da mutunci da Daraja a wajen Allah, aikin da mutum yake ko harkan nemansa ba yana nuna shi makaskanci bane a'a jarabawa ce babu yadda bata zuwa ga Bawa, wanda ya yi hakuri shine zai ga amfanin hakurin wata Rana.

ALLAH kasa mu zamo masu taimakon na kasa da mu Aameen.

Mujahedeen Magaji Abub

ALLAH YASA ALJINNA CE MAKOMAR MU,
03/07/2023

ALLAH YASA ALJINNA CE MAKOMAR MU,

27/08/2020

welcome to shoe

Send a message to learn more

Address

Lagos

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AK Ammar kano posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share