17/08/2021
*COPIED* *01*
*Maiyake kawo idan masoya sunyi rigima shiryawa take gagara, har take jawo rabuwa?*
*Kafin muje abin da yake jawo rashin shiryawar masoyan bayan saɓani, zai matuƙar kyau mu fara da abubuwan da suke jawo ɓatarwa ma tukuna.*
*- idan masoyinki bayason ya ganki da wani ko wata, kika ci gaba da saurararsu zai jawo kuyi rigima.*
*- idan kullum kina cisguna masa zaku ɓata*
*-idan kina jamasa aji dayawa zaku rabu, domin bakowane yake iya jure jan dayawa ba. Wani ajin ana taleshi sai ya tsinke kat.*
*-idan kuna yawan samun saɓanin ra'ayi (abin da yake so kina ƙinsa, ko abin da takeso kullum kasokeshi)*
*-idan kina nuna masa rashin damuwa dashi, ko abin da ya shafeshi.*
*-idan bakya muhimmantar da manyansa ko duk abin da ya ɗaukeshi da muhimmanci*
*-idan kika cika roƙon shi dayawa*
*-idan kina yawan gyara masa kuskurensa. Komai yayi ki nuna bai iya ba ko ba haka yak**ata yayi ba. Shi zai rinƙa ganinsa a raini ne. Kekuma ƙila har ga Allah gyara kikeson yi.*
*- idan kina ɓoye masa wasu abubuwa da ya cancanci ya sani, duk lokacin da ya sani agurin wani ko wata, zaiga ko bashi da kima a gurinki, ko kokuma kina munafuntarsa.*
*-munafunci*
*-ƙarya*
*-mugunta*
*-son kai*
*-cin fuska*
*-cin mutunci*
*-wulaƙanci*
*-raini da rainin wayo ko aji*
*-idan kina nuna masa shifa ana sonshi ne amatsayin wucin gadi. Da original ya fito zaki masgeshi gefe.*
*-idan ya gano ke ba ta aure bace zaku rabu, matuƙar shiɗin da niyyar aure yazo*
*- idan yaga bakya ɗaukar alaƙarku da muhimmanci, ko yanason turowa ki nuna masa a,a*
*- idan ya hanaki abu kiyi ƙememe abin ki.*
(Halayyar yawancin mata a yanzu kenan su sun iya komai kuma ba za'a yi musu gyara ba)
*-idan yaga sirrinsa baya ruƙuwa*
*-idan yaga suna dayawa 'yan takara agurinki kuma shi da gaske yake, amma ko kusa da yazo na farko ma azaɓinki baiyi ba.*
*Dsr*
*Haka kaima idan kana yimata waɗannan abubuwan zasu iya jawo muku rabuwa*
*-taita nuna ta damu dakai, amma kana yimata halin ko in kula*
*-cutarta*
*-ƙarya mai ƙarfin gaske*
*-zagi*
*-musgunawa*
*-cin amana*
*-wulaƙanci*
*- tara mata abokai kala-kala kullum, k**ar wata hajar sayarwa. Ko kace k**ar tana kotu.*
*-ɗaukar ta amatsayin kayan ado, ko rashin kimantata*
*-Rowar tsiya da maƙo da ƙamƙamo kazama banban tsogo kuma matsolo*
*-rashin tura magabata gashi kun ɗau lokaci. Son naka sai ya sane, muddin ta ƙosa tayi aure.*
*-Nuna mata alamomin yaudara ƙiri-ƙiri*
*-Nuna mata kai ɗin ba dagaske kake sonta ba*
*-Rashin kishinta*
*Dsr*
*Waɗannan bubuwan yawanci sune suke jawo rigima da faɗa tsakanin masoya.*
*Idan mun ganosu to mai yake jawo ƙin shiryawar bayan anyi faɗan ko rigimar?*
*Zan cigaba a rubutu na biyu*
*MUNA MARABA DA SHARHI GYARA KO KARIN HASKE GAMI DA TAMBAYA*