Muryar Birni Da Karkara

Muryar Birni Da Karkara Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Muryar Birni Da Karkara, •Fadakarwa. •Tunatarwa. •Waazantawa. •Nishadantarwa. a, Kano.

DAGA SHAFUN DDL HAUSA,,,,,KADDARA: Wani lamari mai tada hankali ya fito fili daga bakin wata mata bazawara, wacce ta bay...
11/09/2025

DAGA SHAFUN DDL HAUSA,,,,,KADDARA: Wani lamari mai tada hankali ya fito fili daga bakin wata mata bazawara, wacce ta bayyana irin mawuyacin hali da ta tsinci kanta a cikinsa tun bayan rasuwar mijinta.

Matar, wacce take da yara shida, biyu maza da kuma mata hudu, ta ce duk da arzikin da mijinta ya bari, hakan bai hana ta shiga cikin wani irin matsi na sha’awa da rudanin rayuwa ba.

A cewarta, duk lokacin da take shirin sake aure ko kuma ta kawo wani bazawari gida, yaranta sukan yi fito-na-fito da ita suna hana ta, suna cewa hakan zai tunasar da su da mahaifinsu. Wannan tsayayya ta yaranta ta jefa ta cikin ruɗani har ta fara neman mafita ta hanyoyi marasa dacewa.

“Na shiga harkar madigo, saboda kawai neman sassauta sha’awar da take damuna. Sau da dama nakan yi amfani da wasu ’yan uwana mata ko kuma abokiyar aiki. Har ma in k**a ɗaki a hotel domin kada yarana ko ’yan uwan mijina su gano sirrina,” in ji matar cikin kuka.

Ta kara da cewa kasancewarta malamar makarantar mata ya sa wani lokaci take amfani da bayanan da take yi wa daliban manya kan rayuwar aure wajen lura da wadanda sha’awarsu ke motsawa, sannan daga baya ta iya jawo su domin biyan bukatunta.

Sai dai matar ta bayyana cewa duk lokacin da ta aikata hakan, sai ta kamu da nadama mai tsanani, ta yi tuba, amma daga baya ta sake komawa. “Kullum nakan yi alwashin daina, amma na kasa. Na gaji da wannan rayuwa,” ta ce cikin hawaye.

A ƙarshe, ta roki malamai da al’umma da su taimaka mata da shawarwari kan yadda za ta guji wannan dabi’a da ta kira mugun aiki, domin samun kariya daga fushin Allah da kuma samun rayuwa mai tsarki.

RAHOTO⭕ Jaridar Maariv ta rawaito daga majiyoyin tsaro na Isra’ila:Firaiminista Netanyahu ba shi da niyyar dakatar da ai...
23/08/2025

RAHOTO

⭕ Jaridar Maariv ta rawaito daga majiyoyin tsaro na Isra’ila:

Firaiminista Netanyahu ba shi da niyyar dakatar da aikin Operation Gideon’s Chariots 2.

Rahoton ya nuna cewa Netanyahu ya kuduri aniyar ci gaba da aikin har zuwa ƙarshe.

An ce ya fahimci cewa ba tare da wannan aiki ba, gwamnatin sa zata iya rugujewa.

Rundunar sojin Isra’ila ta kiyasta cewa yaki a Gaza na iya ci gaba na watanni masu yawa, don haka za a kira dakaru ajin ajiya a hankali.

✍️ Rahoto daga Yaya Babba

YANZU-YANZU: Babban hafson sojan kasar Iran yace; Duk wani hari da zai fuskanci kasar mu Iran, Martanin da zamuYi zai za...
22/08/2025

YANZU-YANZU: Babban hafson sojan kasar Iran yace; Duk wani hari da zai fuskanci kasar mu Iran, Martanin da zamuYi zai zama na ban mamaki ga Duniya. —inji Babban Kwamandan Rundunar Sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Janar Amir Hatami.

Ya bayyana haka ne A Yau Juma’a a; 21 ga Agusta, 20025, A wajen bikin Ranar Masana’antar Tsaro ta Ƙasar Iran.

Mene ne Ra'ayin Ku...?

Sojojin Niger sun sanar da hallaka shugaban kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, Ibrahim Bakoura, wanda aka fi sani da Abo...
21/08/2025

Sojojin Niger sun sanar da hallaka shugaban kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, Ibrahim Bakoura, wanda aka fi sani da Abou Oumaima, a yankin Tabkin Chadi.

📌 Majiyar labari: Bulletin d’information des opérations des FDS (RTN)

Ya k**ata ko wanne ɗan Nijeriya ya koyi dabarun kariyar kai - Chris Musa Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christo...
21/08/2025

Ya k**ata ko wanne ɗan Nijeriya ya koyi dabarun kariyar kai - Chris Musa

Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa ya shawaraci ƴan Najeriya da su laƙanci dabarun kare kai daga haɗurra a matsayin mataki na ko-ta-kwana.

C.G Musa ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels a yau Alhamis, k**ar yadda shafin X na BBC Hausa ya wallafa.

Matsalar tsaro na addabar yankuna da dama na Najeriya, inda masu ɗauke da mak**ai ke kashe mutane tare da tarwatsa su daga muhallansu.

Duk da cewa hukumomi na cewa suna bakin ƙoƙarinsu, amma lamarin na ci gaba da laƙume ɗaruruwan rayuka a yankunan da ake fama da irin waɗannan tashin-tashina, k**ar arewa maso yamma da arewa maso gabas da kuma arewa ta tsakiyar ƙasar.

Lokacin da aka tambayi Christopher Musa kan ko ya k**ata al'umma su koyi dabarun faɗa, ya ce "Ya k**ata mutane su ɗauki wannan tamkar koyon tuƙi ne ko iyo, wannan abu ne da ake buƙata a rayuwa, ko da ana fama da yaƙi ko a'a".

"Ina ganin ya k**ata a wayar da kan kowane ɗan Najeriya kan tsaro a kowane mataki. Kare kai na da matuƙar muhimmanci," in ji Musa.

Ko a ranar Litinin, wasu mahara sun kashe masu ibada aƙalla 28 a wani masallaci da ke karamar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina, arewa maso yammacin ƙasar.

Haka nan a watan da ya gabata masu garkuwa da mutane sun yi wa mutum 38 yankan rago cikin waɗanda suke garkuwa da su a jihar Zamfara mai maƙwaftaka.

Beautiful cabin crew 🌹🌹Scarlett Johansson
16/08/2025

Beautiful cabin crew 🌹🌹
Scarlett Johansson






█▓▒F░O░L░L░O░W▒▓█┊┊┊▕▔╲▂▂▂╱▔▏╭━━╮╭┈╮⠀╭┈╮╭━━╮╰╰╰┃▏╭╮⠀╭╮▕┃╯╯╯┈┃⠀┃▏┈┈▅┈┈▕┃⠀┃┈┃⠀┃▏┈╰┻╯┈▕┃⠀┃┈┃⠀╰█▓▒░M░E░▒▓█  عشر حقائق غير مع...
16/08/2025

█▓▒F░O░L░L░O░W▒▓█
┊┊┊▕▔╲▂▂▂╱▔▏
╭━━╮╭┈╮⠀╭┈╮╭━━╮
╰╰╰┃▏╭╮⠀╭╮▕┃╯╯╯
┈┃⠀┃▏┈┈▅┈┈▕┃⠀┃
┈┃⠀┃▏┈╰┻╯┈▕┃⠀┃
┈┃⠀╰█▓▒░M░E░▒▓█

عشر حقائق غير معروفة عن
1. التأسيس والتاريخ: تأسست BMW ، Bayerische Motoren Werke AG ، في عام 1916 في ميونيخ ، ألمانيا ، حيث أنتجت في البداية محركات الطائرات. انتقلت الشركة إلى إنتاج الدراجات النارية في عشرينيات القرن العشرين وفي النهاية إلى السيارات في الثلاثينيات.
2. الشعار الأيقوني: يتكون شعار BMW ، الذي يشار إليه غالبا باسم "الدائري" ، من حلقة سوداء متقاطعة #الاشاره.*

Address

•Fadakarwa. •Tunatarwa. •Waazantawa. •Nishadantarwa. A
Kano
255255

Telephone

+23488291234

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Birni Da Karkara posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share